Wasanni

Chelsea ta nunawa kocinta halin Damisa

Frank Lampard
Frank Lampard REUTERS/Toby Melville

Kungiyar Chelsea ta kori kocinta Frank Lampard, sakamakon jerin rashin nasarorin da suka fuskanta baya bayan nan a gasar Premier.

Talla

Yayin sanar da matakin hamshakin attajirin da ya mallaki kungiyar ta Chelsea Roman Abramovich, ya ce korar Lampard ba abu ne mai sauki ba, la’akari da girmama shi da yake, a dalilin kyakkyawar alakar da suke da ita. Sai dai kaye da suka rika sha a baya bayan nan ba kuma tare da alamun samun cigaba ba, ya sa dole suka zabi daukar matakin manta sabo.

A shekarar 2019 Lampard wanda tsohon dan wasan Chelsea ne da ya bata gagarumar gudunmawa, ya kulla yarjejeniyar shekaru 3 ta zama kocin kungiyar, wanda kuma a zangonsa na farko ya kai ta ga wasan karshe na gasar cin kofin FA, ta kuma kammala gasar Premier a matsayi na 4.

Yanzu haka dai dai rahotanni na cewa, tsohon mai horas da PSG Thomas Tuchel ake sa ran zai maye gurbin Lampard a kungiyar ta Chelsea, wadda ta gaza lashe wasanni biyar daga cikin takwas da ta fafata karkashin jagorancinsa a baya bayan nan.

A halin yanzu Chelsea ce ta 9 a gasar Premier da maki 29.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.