Wasanni-Kwallon kafa

De Jong ya taimaka wa Barca sun doke Elche duk da rashin Messi

Wasu 'yan wasan Barcelona.
Wasu 'yan wasan Barcelona. Reuters

Duk da rashin Messi, sakamakon horon dakatarwa na wasanni 2 da hukumomi suka ba shi, Barcelona sun doke Elche, da ke samun matsaloli a gasar La ligar Spain har gida da ci 2-0 a yammacin Lahadi, kwallayen da Frenkie de jong da Riqui Puig suka ci.

Talla

A minti na 39 Barcelona suka ci kwallo ta farko, kwallon da ta yi kama da Elche sun ci gida ta hannun Diego Gonzales, amma De Jong wanda shi ya kawo kwallon daga kusurwa ya yi wuf ya taba ta kafin ta ida shiga raga.

Dan wasan gefe na Elche Emiliano Rigoni ya baras da damar farke kwallon da aka saka musu a raga bayan wani kuskure da mai tsaro bayan Barcelona Oscar Mingueza ya tafka, amma mai tsaron ragar Barca, Marc-Andre ter Stegen ya hana shi kaiwa ga gaci.

Barcelona sun yunkuro a minti 89 inda suka kara kwallo ta biyu ta hannun Puig, wanda ya sa wa wata kwallon da De Jong ya kawo kai, abin da ya ba su nasara 4 a jere.

Barcelona na matsayi na 3 a teburin La Ligar Spain da maki 37 a bayan masu jan ragamar gasar, Atletico Madrid, wadanda suka ba su ratar maki 7.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.