Wasanni

PSG ta soma tuntubar Messi

Lionel Messi
Lionel Messi Susana Vera/Reuters

Dan wasan tsakiya na PSG Leandro Paredes, yace kungiyarsa ta soma shirye-shiryen kulla yarjejeniya da kaftin din Barcelona Lionel Messi, mai rike da kambin gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya guda 6.

Talla

A karshen kakar wasa ta bana yarjejeniyar Messi da Barcelona za ta kare, bayan kokarin katse ta da dan wasan yayi a shekarar bara, abinda ya janyo kai ruwa rana tsakaninsa da kungiyar.

Tun kakar wasa ta bara ne kuma ake alakanta Messi da komawa PSG ko kuma Manchester City, kungiyar da a waccan lokacin har ta tattauna da maihafin tauraron dan wasan.

Kwallaye 14 Messi ya ci wa Barcelona a dukkanin wasannin da ya buga mata a kakar wasa ta bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.