Wasanni-Kwallon kafa

'Yan wasana ba su cancanci doke Man United ba - Klopp

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool  Jurgen Klopp.
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp. REUTERS/Charles Platiau

Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce ‘yan tawagarsa ba su taka rawar da za ta kai su ga doke Manchester United ba, bayan da suka sha kashi 3-2 a zagaye na 4 na gasar cin kofin Kalubalen Ingila ta FA a jiya Lahadi.

Talla

Liverpool ne dai suka fara saka kwallo a raga ta hannun Mohamed Salah, a wasan da aka buga a filin Old Trafford na Manchester United, kuma Salah din ne ya farke wa Liverpool kwallo ana 2-1, bayan da Mason Greenwood da Marcus Rashford suka sanya United a gaban Liverpool.

Daga karshe Bruno Fernandes ya yanke hukunci, ta wajen saka wata kwallo a ragar Liverpool a minti na 78, ta wajen wani bugun tazara da ya gagari mai tsaron raga Alisson, duk da cewa daga nesa aka bugo mai kwallon.

Klopp ya bayyana farin cikinsa da bangarori da dama na irin rawar da tawagarsa ta taka, amma kuma yana jin ‘yan wasansa sun tafka kurakurai da dama a mahimman lokuta.

Ya bayyana takicin yadda ‘yan wasan nasa suka baras da damammakin cin kwallo a wasan da ya kamata a ce sun samu nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.