Laporta ya zargi PSG da rikita lissafin Barcelona saboda Messi
Wallafawa ranar:
Joan Laporta, dan takarar dake kan gaba tsakanin masu neman darewa kujerar shugabancin Barcelona, ya zargi PSG da haddasawa kungiyar rudani, sakamakon soma tuntubar kaftin dinsu Lionel Messi.
A makon jiya daraktan wasannin PSG Leonardo ya ce kulla yarjejeniya da manyan ‘yan wasa irinsu Messi shi ne burinsu, yayin da kuma a farkon makon nan, dan wasan tsakiya na kungiyar ta PSG Leandro Paredes yace tuni suka soma tuntubar kaftin din na Barcelona don haka a yanzu wuka da nama na hannunsa.
A karshen kakar wasa ta bana yarjejeniyar Messi da Barcelona za ta kare, bayan kokarin katse ta da dan wasan yayi a shekarar bara, abinda ya janyo kai ruwa rana tsakaninsa da kungiyar.
Tun kakar wasa ta bara ne kuma ake alakanta Messi da komawa PSG ko kuma Manchester City, kungiyar da a waccan lokacin har ta tattauna da maihafin tauraron na dan wasan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu