Wasanni

Mbappe ya ki fayyace makomar yarjejeniyarsa da PSG

Kylian Mbappé
Kylian Mbappé Reuters/Eric Gaillard

Kungiyar PSG ta soma tuntubar dan wasanta Kylian Mbappe kan bukatar sabunta yarjejeniyarsu dake shirin karewa.

Talla

A baya bayan nan ne dai Mbappe ya bayyana cewa har yanzu bai yanke shawarar cigaba da zama a PSG ba, ko kuma ya sauya sheka zuwa wata kungiyar, wadda ake kyautata zaton ba za ta wuce Real Madrid ba.

Sai dai a bangaren Madrid da ta jima tana bibiyar bajintar dan wasan, zai yi wahala ta iya kulla yarjejeniya dashi a nan kusa, la’akari da kalubale har kashi biyu dake gabanta.

Kalubale na farko dai shi ne raguwar kudaden shigar da take samu saboda annobar Korona, sai kuma bashin euro miliyan 570 da ta karba domin sake fasalin filin wasanta na Santiago Bernabeu, wanda za ta fara biya a farkon shekarar 2022, kuma kawo yanzu euro miliyan 100 ya zo hannun kungiyar, yayin da ragowar kuma sai watan Yunin shekarar ta 2022.

Kawo yanzu dai Mbappe na karbar albashin euro miliyan 21 ne duk shekara a PSG.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.