Wasanni-Kwallon kafa

Kudi ba za su rudi Messi ya raba gari da Barcelona ba- Koeman

Dan wasan gaba na Barcelona Lionel Messi.
Dan wasan gaba na Barcelona Lionel Messi. REUTERS/Albert Gea

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Ronald Koeman ya ce baya tunanin kudi zai rudi dan wasansa kuma Kaftin din tawagar Lionel Messi, don sauya sheka dai dai lokacin da Club din ya fada cikin matsalar kudi.

Talla

Koeman wanda ke wannan batu gabanin karawar Barcelona ta yau Laraba da Rayo Vallecano karkashin gasar cin kofi Copa del Rey, Kocin ya ce Messi na cikin tawagar da za ta kara a wasan, wanda ke matsayin wasansa na farko bayan dakatarwar wasanni 2 da ya fuskanta yayin wasan karshe na cin kofin Spanish Super Cup sakamakon sa’insa da alkalin wasa.

Koeman a wani taron manema labarai, ya musanta rade-radin cewa Messi zai sauya sheka a nan kusa, inda ya ce dan wasan yana matukar jin dadin taka leda da Barcelona a yanzu, kuma a shirye ya ke ya bayar da dukkanin gudunmawar da ake bukata.

Barcelona dai cikin bayanan da ta fitar a farkon makon nan ta bayyana yadda ta ke fama da bashin fiye da dala biliyan guda, matakin da wasu bayanai ke cewa yanzu haka Club din ya gaza biyan ‘yan wasansa wasu hakkokinsu daya kamata a basu tun cikin watan Disamba wanda yanzu sai a Fabarairu za su karba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.