Wasanni-Kwallon kafa

RB Leipzig na fargabar haduwarta da Liverpool- Nagelsman

'Yan wasan RB Leipzig yayin karawarsu da Monaco.
'Yan wasan RB Leipzig yayin karawarsu da Monaco. REUTERS/Eric Gaillard

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta RB Leipzig Julian Nagelsmann ya ce ya na cike da fargabar haduwar tawagarsa da Liverpool karkashin wasannin cin kofin zakarun Turai.

Talla

A kalamansa yayin taron manema labarai gabanin karawar Liverpool da RB Leipzig a Budapest gobe Talata, Nagelsmann ya ce rashin abin kirkin da Liverpool ke yi a wasannin Firimiya na baya-bayan nan ba shi zai basu kwarin gwiwar iya doketa a karawar ba.

Liverpool na shirin yin tattaki zuwa Budapest biyo bayan rashin nasara a wasanni 9 na Firimiya ciki har da rashin nasara 3 a jere.

Ko a Asabar din da ta gabata Jurgen Klopp ya amsa cewa ba shi da tabbacin Liverpool za ta iya kare kambunta na Firimiya bayan canjaras dinta da Leicester City wanda ya kara tazarar da ke tsakaninta da Manchester City jagora zuwa maki 13.

A bangare guda RB Leipzig na matsayin ta 2 ne a teburin Bundesliga kasa da Bayern Munich mai rike da kambun na zakarun Turai.

Nagelsmann ya ce za su yiwa karawar dukkan shirin da ya kamata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.