Wasanni

PSG ta yiwa Barcelona wanka da ruwan sanyi - Koeman

Mai horas da kungiyar Barcelona Ronald Koeman
Mai horas da kungiyar Barcelona Ronald Koeman REUTERS/David Klein/File Photo

Kocin Barcelona Ronald Koeman ya ce ba shakkah PSG ta yi musu wanka da ruwan sanyin da ke bayyana gaskiyar halin da suke ciki na matsalolin da suka tilasta musu fuskantar kalubale.

Talla

Koeman ya bayyana haka ne yayin da yake tsokaci kan lallasa su da PSG tayi da 4-1 a haduwarsu ta farko a zagayen gasar Zakarun Turai na biyu.

Dangane da batun makomarsa kuwa, Koeman ya kuma ce batun tunanin zai ajiye aiki ma bai taso ba, inda ya bayyana muhawarar da wasu ke yi kan batun a matsayin rashin hankali.

Yayin wasan na jiya Talata dai matashin dan wasan PSG Kylian Mbappe ya nuna kansa inda ya ci kwallaye 3, yayin da Moise Kean ya ci 1, a bangaren Barcelona kuwa Messi ne ya ci mata kwallon guda daga bugun fanereti.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.