Wasanni

Solskjaer ya sha alwashin dage kofin Europa a bana

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Ole Gunnar Solskjaer.
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Ole Gunnar Solskjaer. Reuters/Andrew Boyers

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya yi ikirarin cewa tawagarsa na cikin gasar Europa ne kadai don gyaran kura-kuren da ta tafka a kakar da ta gabata tare da dage kofin wanda yakamata ace ya isa gidanta tun a kakar da ta gabata.

Talla

Solskjaer na wannan batu bayan nasarar Manchester United kan Real Sociedad a karawarsu ta jiya Alhamis da kwallaye 4 da nema yayin wasan wanda ya gudana a Turin, zagayen kungiyoyi 16.

Ko a bara Manchester United ta kai zagayen karshe na wasannin cin kofin amma kuma ragargazar da Sevilla ta yi mata ya tilasta mata komawa gida ba tare da kofin ba a wasanni gab da na karshe.

A wasan na jiya dai United ta samu kwallayen na ta hudu ne ta hannun Bruno Farnandez da ya zura kwallo 2 kana Marcus Rashford ya zura kwallo guda sai kuma kwallon Daniel James a gab da karkare wasa.

A kalaman Solskjaer wanda yanzu haka tawagarsa ke matsayin ta biyu a teburin Firimiya, ko shakka babu wannan karon kungiyar ta sa baza ta yi sakacin rasa kofin ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI