Wasanni-Kwallon kafa

Enyimba da Pirates za su farfado da hamayyar da ke tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu

Alamar hukumar kwallon kafa ta Afrika.
Alamar hukumar kwallon kafa ta Afrika. CAF

Orlando Pirates da Enyimba za su sabanta gagarumar hamayyar kwallon kafar da ke tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu bayan da jadawalin gasar kwallon kafa ta nahiyar Afrika ta CAF Confederation Cup da aka yi a birnin Alkahira a Litinin ya hada kungiyoyin 2 a rukuni na A.

Talla

Wasu kungiyoyin arewacin Afrika kamar su, Entente Setif ta Algeria da Al Ahly Benghazi ta Libya, su ne sauran kungiyoyin da jadawalin ya nuna suna cikin rukuni guda da kungiyoyin na Najeriya da Afrika ta Kudu.

Enyimba da Setif sun taba lashe gasar zakarun nahiyar Turai har sau 2, yayin da Pirate ta lashe sau daya, Bengazi kuwa ta taba yunkurawa zuwa matakin kungiyoyi 16 saboda ba za su iya wasa a gida ba sakamakon dalilai na tsaro.

Masu rike da kofin, Renaissance Berkane na Morocco na rukuni na B tare da JS Kabylie na Algeria, Coton Sport na Cameroon da NAPSA Stars na Zambia.

Za a samu kungiyoyin Tunisa har 2 a rukunin C idan Etoile Sahel suka doke Young Buffaloes na eSwatini a wasa zubi na 2 da aka jinkirta, bayan da a zubi na farko suka yi nasara 2-1 a can eSwatini.

Wadanda suka yi nasara za su hade da CS Sfaxien na Tunisia, wadanda sau 3 suka taba lashe kofin CAF Confederation, da kuma kungiyoyi 2 daga yammacin Afrika, Salitas na Burkina Faso da ASC Jaraaf na Senegal.

Raja Casablanca na Morocco da Pyramids na cikin rukuni na D tare da Nkana na Zambia, wadanda ba su taba yin rashin nasara a gida ba, a wasanni har 64 na CAF, haka kuma, wadanda suka yi nasara tsakanin Namungo na Tanzania da Primeiro Agosto na Angola.

A ranar Laraba, 10 ga watan Maris za yi wasannin farko a matakin rukuni, haka kuma za a yi wasannin karshe na matakin rukuni a ranar Laraba, 28 ga watan Afrilu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI