Wasanni-Kwallon kafa

Manchester City za ta tsallake zagayen kungiyoyi 16 -Gundogan

'Yan wasan Manchester City.
'Yan wasan Manchester City. Reuters/Andrew Yates

Dan wasan tsakiyar Manchester City Ilkay Gundogan ya ce yanayin yadda suka fice daga gasar cin kofin zakarun turai a bara ba zai shafi kokarinsu na tsallake matakin a bana ba, inda ya ce yana da kwarin gwiwar tawagar ta sa ta tsallake zagayen kungiyoyi 16 cikin sauki.

Talla

Gundogan da ke wannan batu gabanin karawarsu da Borussia Mochengladbach yau laraba a filin wasa na Budapest da ke Hungary, karkashin gasar ta zakarun Turai wasan farko a zagayen kungiyoyi 16, ya ce ficewar ta bara har yanzu tana musu radadi dalilin da ya sanya su shan alwashin kaiwa ga nasara a wannan karon.

ManCity jagora a Firimiyar Ingila a baran ita ta fitar da Real Madrid daga gasar amma kuma itama Lyon ta Faransa ta yi waje da ita bayan doketa da kwallaye 3 da 1 a Lisbon.

Tawagar ta Guardiola wadda yanzu haka ke kan ganiyarta bayan nasara a wasanni 18 a jere, ko a jiya Talata mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Mochengladbach Marco Rose sai da ya bayyana fargaba kan haduwar ta su ta yau, yana mai cewa tawagarsa ta shirya tsaf don karon batta da zakakuran ‘yan wasa na Duniya.

Sai dai za a iya cewa itama Gladbach din ba kanwar lasa bace la’akari da yadda ta iya nasarar tsallake wasannin rukuni duk da kasancewar manyan kungiyoyi a rukunin da suka kunshi Real Madrid, Inter Milan da kuma Shaktar Donetsk, amma kuma ta nuna bajintar yin zarra.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI