Kwallon Kafa-Gasar Zakarun Turai

An yi mana kisan kai a wasanmu da Real Madrid-Gasperini

Kocin Atalanta Gian Piero Gasperini ya fusata da dukan da Real Madrid ta yi musu a gasar zakarun Turai.
Kocin Atalanta Gian Piero Gasperini ya fusata da dukan da Real Madrid ta yi musu a gasar zakarun Turai. MIGUEL MEDINA AFP/File

Kocin Atalanta Gian Piero Gasperini ya bayyana bacin ransa kan abin da ya kira kisan kai a kwallon kafa bayan ‘yan wasansa sun shafe tsawon mintina 70 ba tare da dan wasa guda ba da aka ba shi jan kati a karawar da Real  Madrid ta yi musu ci daya mai ban haushi a gasar zakarun Turai.

Talla

A cikin minti na  17, alkalin wasa ya bai wa Remo Freuler jan kati bayan ya harde kafar Ferland Mendy a gab da da’irar mai tsaren ragar Atalanta.

Kocin na Atlanta ya sake shiga cikin bakin ciki bayan Mendy ya yi nasarar jefa kwallon daya tilo a ragarsu a minti na 86, wato ana sauran minti hudu a tashi wasan.

Kocin ya ce, abin takaici ne alkalin wasa ya kasa banbance tsakanin keta da kuma tunkara, yana mai cewa, muddin alkalin wasa ba ya iya fahimtar keta ko kuma tunkara, to ya nemi wani aikin daban, amma ba alkalancin wasa ba.

Real Madrid ta buga wasan  na jiya ba tare da  wasu daga cikin zaratanta ba da ke jinya, cikinsu kuwa har da Karim Benzema wanda ya fi yawan kwallaye da Sergio Ramos da Eden Hazard da Dani Carvajal.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI