Wasanni - Ingila

Okocha ya bukaci Salah ya sauya sheka daga Liverpool zuwa Barcelona

Tauraron kungiyar Liverpool Muhammad Salah
Tauraron kungiyar Liverpool Muhammad Salah AP - Phil Noble

Tsohon kaftin din tawagar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles Austin Jay-Jay Okocha ya shawarci tauraron Liverpool Muhammad Salah da ya gaggauta rabuwa da kungiyar, ya kuma sauya sheka zuwa Barcelona.

Talla

Shekaru biyu suka rage yarjejeniyar Salah ta kare da Liverpool, wanda aka dade ana alakantawa da shirin barin kungiyar, bayan da wasu majiyoyi suka nuna cewar, dagantaka tayi tsami tsakaninsa dan wasan da kocin kungiyar at Liverpool Jurgen Klopp.

Zalika a baya bayan nan, yayin Sala ya bayyana Real Madrid da Barcelona a matsayin kungiyoyin da babu kamarsu a duniya

Yanzu haka dai Salah ne ke kan gaba wajen yawan kwallaye a tsakanin takwarorinsa a gasar Premier bayan jefa 17, yayinda kuma a ya ci jumilar 24 cikin wasanni 34 da ya bugawa kungiyar tasa a kakar wasa ta bana.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.