Wasanni

Caster Semenya na son kotu ta janye mata haramcin tseren mita 400

Caster Semenya 'yar tseren Afrika ta kudu.
Caster Semenya 'yar tseren Afrika ta kudu. AFP/Archives

Zakarar tseren gudun mitoci 400 ta gasar Olympic ‘yar Afrika ta Kudu Caster Semenya, ta shigar da kara gaban kotun kare hakkin dan adam ta kungiyar tarayyar Turai, inda take kalubalantar matakin hukumar wasannin motsa jiki na haramtawa ‘yan wasa irinta masu kirar karfi tamkar maza shiga wasanni motsa jiki na mata.

Talla

Tun a shekarar 2018 ne dai, hukumar wasannin motsa jiki ta duniya ta haramtawa Semenya da sauran mata masu motsa jiki da kirar su ta bambamta da mata shiga wasannin tseren gudu na mitoci 400, muddin basu sha magungunan da za su rage musu karfi ba.

Tun a waccan lokacin ne kuma Semenya ta ruga kotun sauraron kararrakin wasanni da kuma kotun kolin kasar Switzerland ton kalubalantar hukuncin takaita musu shiga wasannin motsa jiki na mata, amma tayi rashin nasara.

Fitacciyar ‘yar tseren ta sha alwashin shiga gasar gudun mitoci 200 a gasar Olympics ta 2020,a wadda aka dage ta zuwa shekarar bana saboda annobar Korona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI