Wasanni

Atletico Madrid ta kama hanyar lashe gasar Liliga

Dan wasan gaba na Atletico Madrid Luis Suarez yayin murnar cin kwallo a karawarsu da Celto Vigo.
Dan wasan gaba na Atletico Madrid Luis Suarez yayin murnar cin kwallo a karawarsu da Celto Vigo. PIERRE-PHILIPPE MARCOU AFP/Archives

Atletico Madrid dake jan ragamar teburin Liligar kasar Spain ta kara tazarar maki 5 ga mai biye mata Barcelona, bayan doke Villarreal da ci 2-0 a waje.

Talla

Atletico, na kokarin lashe gasar ta Sipaniya a karon farko tun gasar shekararar 2013-14, bayan da dan wasan Villarreal Alfonso Pedraza ya zurawa ragarsu kwallo, Kafin daga bisani Joao Felix ya kara kwallo na biyu.

Sakamakon ya ba su maki biyar a gaban Barcelona da ke matsayi na biyu, da maki shida a gaban Real Madrid, wacce Atletico za ta karbi bakunci a wasan hamayya ranar 7 ga watan Maris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.