Wasanni

Gara na rasa wasannin Olympics da in karbi rigakafin korona - Blake

Shahararren dan wasan tseren duniya dan kasar Jamaica Yohan Blake
Shahararren dan wasan tseren duniya dan kasar Jamaica Yohan Blake AP - Markus Schreiber

Shahararren dan wasan tseren duniya dan kasar Jamaica Yohan Blake ya bayyana matsayin na adawa da rigakafin cutar coronavirus bayan ya yi tsokaci cewa zai gwammace ya rasa halartar gasar wasannin Olympics ta Tokyo 2020 da a yi masa allurar.

Talla

Yohan Blake, wanda ya ci azurfa a tseren mita 100 da 200 a Landan a shekarar 2012 da kuma zinare a gudun mita 100  a Rio shekarar 2016, ya yi wadannan kalaman ne bayan da masu shirya gasar a Japan suka bayyana shirinsu na tabbatar lafiyar ‘yan wasa.

Amma dan wasan mai shekaru 31 ya bayyanawa jaridar wasanni ta Jamica Gleaner karara, cewa "Har yanzu ina kan bakata daram, ba na son allurar a cewarsa, kuma yace yana da nashi dalilai na kin rigakafin.

Masu shirya gasar sun ce  'yan wasa ba za su bukaci a yi musu allurar rigakafi a Tokyo ba, amma rashin bin ka’idoji kariya daga koronar zai sa a kori dan wasa daga gasar.

Daga cikin dokokin da aka sanya akwai haramcin rera waka da rungumar juna da musabaha. Haka zalika 'yan wasa dole ne su guji haɗa jiki a sansanin na Olympic.

A ka'ida, wannan yana nufin 'yan wasa ba za su iya yin jima'i a ba – wani lamari da galibi yake  faruwa a irin wannan yanayi - kuma wataƙila ba za a ba su izinin rera taken ƙasarsu a kan mimbari ba, kodayake da wuya a aiwatar da hakan.

Za a rika yiwa ‘yan wasa gwajin korona bayan kowane kwanaki hudu, kana ‘yan wasa da jami'ai zasu iya barin masaukinsu ne kawai don zuwa wuraren da aka tsara kuma ba za su iya amfani da motocin haya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.