Wasanni

Liverpool za ta karkare Firimiyar bana a 'yan hudun saman teburi- Klopp

Manajan kungiyar Liverpool Jurgen Klopp.
Manajan kungiyar Liverpool Jurgen Klopp. POOL/AFP

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya ce har yanzu yana sa ran tawagarsa ta iya kai labari wajen karkare wasannin Firimiyar bana a ‘yan 4 saman teburi.

Talla

Klopp wanda ke wannan batu bayan nasarar Liverpool kan Sheffield United da kwallaye 2 da nema wanda ya bata damar rage ratar da ke tsakaninta da ‘yan hudun na saman teburi ya ce yana da yakinin tawagar ta sa ta bada mamaki duk da jerin matsalolin da suka dabaibayeta a wannan kaka.

Kwallon da Curtis Jones mai shekaru 20 ya zura a ragar Sheffield ta zama kwallo ta dubu 7 da Liverpool ta zura inda ya bata damar kafa tarihin zama kungiya ta biyu da ta kai wannan mataki bayan Everton wadda kawo yanzu ke da kwallaye dubu 7 da 108 da ta zurawa kungiyoyin Ingila.

A cewar Klopp da dama na rubuce rubuce da ke ganin ko shakka babu Liverpool za ta tsinci kanta a Europa cikin kaka mai zuwa, amma shi yana da kwarin gwiwar su iya kamala kakar wasan a ‘yan hudun saman teburi ta yadda za sus amu sukuni shiga gasar cin kofin zakarun Turai.

Yanzu haka dai Liverpool na matsayin ta 6 ne a teburin Firimiyar da maki 43, ko da ya ke tazarar maki 4 ne tsakaninta da West Ham wadda ke matsayin ta 4 a teburin na Firimiya kuma gurbin da Klopp ke hari kenan.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.