Wasanni

Everton za ta yi gogayya da Liverpool wajen neman gurbin ta 4 Firimiya

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Everton Carlo Ancelotti.
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Everton Carlo Ancelotti. POOL/AFP

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Everton Carlo Ancelotti ya ce fatansa ganin tawagarsa ta shiga rukunin ‘yan hudun Firimiya, bayan nasararta kan Southampton da kwallo 1 mai ban haushi a daren jiya Litinin.

Talla

A cewar Ancelotti tun bayan nasararsu kan babbar abokiyar dabinsu Liverpool ranar Alhamis din da ta gabata, ya fara samun kwarin gwiwar kai Everton ga rukunin na ‘yan hudun saman Teburi.

Yanzu haka dai Everton na da wasa daya a hannu yayinda ta ke kan-kan-kan da Liverpool, tazarar maki 1 kuma cal tsakaninta da Chelsea, kuma matukar ta yi nasara a karawar ranar Alhamis dinnan da za ta karbi bakoncin West Brom, kai tsaye za ta shige gaban Chelsea a matsayin ta 5 da Liverpool da ke matsayin ta 6 har ma da ita kanta West Ham da ke matsayin ta 4.

A bangare guda karawar Liverpool da Chelsea a dai ranar ta Alhamis yayin wasan da zai gudana a Anfield shi zai fayyace wadda za ta matsa kusa da West ham koma ta karbe matsayin na West Ham a teburin Firimiya, la’akari da yadda dukkaninsu ke harin gurbin

Sai dai Ancelotti ya ce yana da kwarin gwiwar iya kaiwa wannan mataki wanda Club din ya jima bai kai shi ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.