Zlatan Ibrahimovic zai rasa karawar AC Milan da Manchester United
Wallafawa ranar:
Da yiwuwar dan wasan gaba na AC Milan Zlatan Ibrahimovic ya rasa damar taka leda a karawar kungiyarsa da Manchester United karkashin gasar Europa cikin mako mai kamawa sakamakon raunin da ya samu a kafarsa.
Sanarwar da AC Milan ta fitar ta ce raunin na Zlatan zai tilasta masa jinyar makwanni akalla 3 wanda ke nuna zai rasa karawar tawagar ta sa da tsohuwar kungiyarsa Manchester United a ranakun 11 da 18 ga watan nan.
Zlatan mai Shekarau 39 wanda ya zurawa tsohuwar kungiyar ta sa kwallaye 29 a wasanni 53 ko a karawarsu da Roma cikin makon da ya gabata sai da aka sauya shi ana tsaka da wasa saboda raunin da ya samu a kafarsa, duk da cewa hakan bai hana AC Milan nasara kan Roma da kwallaye 2 da 1 ba.
Zuwa yanzu kwallaye 16 Zlatan dan Sweden ya zurawa AC Milan a wasanni 21 cikin wannan kaka inda yanzu haka kungiyar tasa ke matsayin ta 2 a teburin Serie A tazarar maki 4 tsakaninta da jagora Inter Milan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu