Wasanni

Cristiano Ronaldo ya zama dan wasa mafi bajinta a tarihin kwallo

Dan wasan gaba na Juventus criatiano Ronaldo.
Dan wasan gaba na Juventus criatiano Ronaldo. Isabella BONOTTO AFP

Dan wasan gaba na Juventus Cristiano Ronaldo ya sake nuna bajinta a karawar tawagarsa da Spezia jiya Talata karkashin gasar Serie A ta Italiya inda ya ingiza tawagar tasa ta yi nasara da kwallaye 3 da nema.

Talla

Dan wasan na Portugal da ya taka leda a Real Madrid da Manchester United bajintar da ya sake nunawa a wannan kaka, ta mayar da shi dan wasa daya tilo da ya iya zura kwallaye 20 ko fiye cikin kowacce kaka a manyan gasannin Turai 5 cikin shekaru 12 da suka gabata.

Ronaldo wanda ya zura kwallon ta sa a minti na 83 abokanan wasansa Alvaro Morata da Federico Chiesa ne suka zura kwallon ta daya da ta biyu, ko da ya ke har yanzu tawagar tasa na matsayin ta 3 da maki 49 kasa da Inter Milan a matsayin jagora da maki 56 sai kuma AC Milan da a matsayin ta 2 da maki 52.

 Cristiano Ronaldo mai shekaru 36 ya kafa tarihin zama dan kwallo 1 tilo a ban kasa mafi zura kwallo a fagen tamaula ta Duniya.

A cikin shekaru 9 da ya shafe yana murza tamaula a Real Madrid, Ronaldo ya zura kwallaye akalla 25 a kowace kaka, inda sau uku ma ya ke cin kwallaye 40  a gasar ta Spain.

Haka zalika tun bayan da ya koma Juventus, Ronaldo bai yi kasa a gwiwa ba, saboda a cikin kaka 2 na farko da ya yi a kungiyar ya zura kwallaye 52.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.