Wasanni

Barcelona ta kama hanyar lashe kofin gasar Copa del Rey na 31

'Yan wasan Barcelona yayin murnar samun nasara kan kungiyar Sevilla a wasan kusa da na karshe na gasar Copa del Rey. 3/3/2021.
'Yan wasan Barcelona yayin murnar samun nasara kan kungiyar Sevilla a wasan kusa da na karshe na gasar Copa del Rey. 3/3/2021. AP - Joan Monfort

Barcelona ta goge kwallaye biyun da Sevilla ta zura mata a zagayen farko na wasansu a gasar Copa del Rey bayan da a ranar Laraba ta samu nasara da kwallaye 3-0 a zagaye na biyu da suka fafata.

Talla

Yanzu haka a jumulce Barcelona  na da kwallaye uku, yayin da Sevilla ke da kwallaye biyu, wato idan aka hada da sakamakon wasansu na farko kenan.

Barcelona wadda ke harin lashe kofin gasar Copa Del Rey karo na 31, za ta fafata da kodai da Athletico Bilbao ko kuma Levante a wasan karshe.

Koda yake Barcelona ta yi wasan ne a cikin wani yanayi na jimamin samamen da jami’an tsaro suka kai Camp Nou, yayin da aka kama tsohon shugabanta, Josep Maria Bartomeu saboda zargin cin hanci da rashawa.

A ranar Lahadi mai zuwa ne kungiyar za ta zabi sabon shugabanta, inda ‘yan takara uku ke fafatawar neman mukamin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.