Wasanni-Ingila

Real Madrid ce kawai za ta iya fayyace makomar Bale - Mounrinho

Dan wasan Real Madrid Gareth Bale dake zaman aro a kungiyar Tottenham.
Dan wasan Real Madrid Gareth Bale dake zaman aro a kungiyar Tottenham. AP - Daniel Leal Olivas

Kocin Tottenham Jose Mouinho yace, kungiyar Real Madrid ce kawai za ta iya fayyace makomar Gareth Bale, kodai ya ci gaba da zama a Tottenham ko kuma ya tarkata komatsansa a kaka mai zuwa.

Talla

Bale mai shekaru 31 na zaman aro ne yanzu haka a Tottenham, a daidai lokacin da ya rage shekara guda yarjejeniyarsa da Real Madrid ta kare. 

A baya bayan nan dai tauraron Bale ya soma yin haske a kungiyar ta Tottenham inda yake zaman aro, la’akari da rawar da ya taka yayin wasan da suka lallasa Burnley da kwallaye 4-0, inda ya ci 2. Daga ciki.

Sai dai duk da kokarin na Bale mai horas da shi Mourinho ya ce, Bale fa ba dan wasan Tottenham bane, don haka Real Madrid ce kawai ta san yadda za ta yi da shi a cewarsa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.