Wasanni-Ingila

An sake lallasa Liverpool a gasar Firimiya

'Yan wasan kungiyar Fulham yayin murnar samun nasarar doke Liverpool da 1-0 a gasar Firimiya.
'Yan wasan kungiyar Fulham yayin murnar samun nasarar doke Liverpool da 1-0 a gasar Firimiya. AP - Paul Ellis

Alamu na kara tabbata kan cewa ba lallai bane kungiyar Liverpool ta kwashi wani abin azo a gani kakar wasa ta bana a gasar Premier League, bayan kayen da ta sha da 1-0 a hannun Fulham yayin fafatawarsu a ranar Lahadi.

Talla

Karo na 6 kenan da Liverpool ke shan kaye a jere a wasannin da ta buga a baya bayan nan.

Wani karin koma baya ga masu rike da kofin gasar Firimiyar, shi ne idan Chelsea dake mataki na hudu ta samu nasarar doke Everton a wasan da za su buga a yau. Muddin Chelsea ta lashe wasan nata, za ta kara tazarar da ta baiwa Liverpool zuwa maki 7 sabanin 4 dake tsakaninsu a yanzu haka.

Rabon da Liverpool ta nuna karsasshi a wasanninta tun gaf da bikin ranar Kirsimeti a karshen shekarar 2020, kalubalen da ake dangantawa da jinyar raunukan da wasu fitattun ‘yan wasan kungiyar ke yi.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.