Wasanni - Ingila

Rangers ta lashe kofin Firimiyar Scotland na farko cikin shekaru 10

Mai horas da kungiyar Rangers Steven Gerrard, yayin wasan da suka fafata da Benfica a rukuni na 4 na gasar Europa. 5/11/2020.
Mai horas da kungiyar Rangers Steven Gerrard, yayin wasan da suka fafata da Benfica a rukuni na 4 na gasar Europa. 5/11/2020. AP - Armando Franca

Tsohon dan wasan Liverpool da ya kasance tauraronta Steven Gerrard, ya samu nasarar jagorantar kungiyar Rangers ga lashe kofin gasar kwallon kafar Scotland bayan shafe shekaru da dama kungiyar da magoya bayanta na dakon ganin nasarar.

Talla

Karo na farko kenan da Rangers ta lashe kofin na Firimiyar Scotland cikin shekaru 10.

A shekarun baya dai kungiyar Celtic ce ta yi fice a gasar kwallon Scotland inda ta lashe kofuna 9 a jere, yayin da kuma a jumlace ta lashe kofuna daban daban a wasannin kwallon kafar kasar har 20 tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020.

Baya ga tarihin jagorantar Rangers zuwa ga lashe kofin farko cikin shekaru 10 da yayi, Steven Gerrard ya kuma zama kocin farko da hukumar gudanarwar kungiyar ta baiwa damar jagorantar ta zuwa kakar wasa ta uku, bayan gaza samun lashe gasar Firimiyar ta Scotland da yayi a tsawon shekaru 2 da yayi yana horas da su.

Steven Gerrard a zamanin da yake dan wasa a kungiyar Liverpool. Gerrard yayi tsalle ne bayan jefa kwallo ta 3 a ragar kungiyar Luton, yayin fafatawarsu a gasar cin kofin FA. 15/1/2008.
Steven Gerrard a zamanin da yake dan wasa a kungiyar Liverpool. Gerrard yayi tsalle ne bayan jefa kwallo ta 3 a ragar kungiyar Luton, yayin fafatawarsu a gasar cin kofin FA. 15/1/2008. AP - JON SUPER

Gerrard dai bai taba samun nasarar lashe kofin gasar Firimiyar Ingila ba a tsawon lokacin da ya shafe yana haskawa a Liverpool a matsayin dan wasa, sai dai nasarar da ya samu a Rangers ta sanya wasu tunanin cewa zai iya maye gurbin kocin Liverpool na yanzu Jurgen Klopp da zarar ya raba gari da kungiyar, sakamakon jerin rashin nasarorin da take fuskanta a baya bayan nan a karkashin jagorancinsa.

A baya bayan nan Mai horas da Liverpool Jurgen Klopp ya shaidawa hukumar gudanarwar kungiyar cewa, suna da damar yanke hukuncin fara lalubane wanda zai maye gurbinsa ko kuma bashi damar cigaba da aikinsa.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.