Wasanni-Spain

Real Madrid ta tsallake rijiya da baya a gasar La Liga

Dan wasan Real Madrid Karim Benzema yayin rama kwallon da Atletico Madrid ta jefa musu a gasar La Liga.
Dan wasan Real Madrid Karim Benzema yayin rama kwallon da Atletico Madrid ta jefa musu a gasar La Liga. AP - Manu Fernandez

Real Madrid ta tsallake rijiya da baya, a gasar La Liga ta Spain yayin wasan da suka fafata da Atletico Madrid, wanda suka tashi kunnen doki 1-1.

Talla

Luis Suarez ne ya fara ci wa Atletico Madrid kwallo kafin kaiwa ga tsakiyar zangon farko na mintuna 45, ana gaf da karkare wasan ne kuma Karim Benzema ya ramawa Real Madrid.

Sai dai sakamakon wasan ya baiwa Barcelona damar matsawa kusa da Atletico Madrid da a yanzu haka take jagorantar gasar La Liga da maki 59.

Bayan nasarar da ta samu kan Osasuna da 2-0 a karshen mako, a yanzu Barcelona ke matsayi na biyu da maki 56, yayin da Real Madrid ke biye da ita a matsayi na 3 da maki 54.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.