Yarima Mosaad na Saudiya zai saye club din kwallon kafar Faransa Chateauroux
Wallafawa ranar:
Hamshakin Miliyoniyan Saudiya kuma yariman masarautar kasar, Abdullah Bin Mosaad yace zai sayi kulob din Chateauroux na Faransa.
Mutumin da ya bayyana kansa amatsayin masoyin "kudi da wasanni", na gab da zama mamallakin kungiyar kungiyar Chateauroux dake buga wasannin rukuni na biyu a Faransa.
Tuni Yarima Bin Mosaad mai shekaru 56 da ya mallaki kungiyoyin da ke gwagwarmayar Firimiya kamar su Sheffield United, Beerschot a Belgium, Kerala United na Indiya da Al Hilal United a Hadaddiyar Daular Larabawa, nan ba da daɗewa ba zai mallaki sabuwar ƙungiya a Faransa
A hirar da yayi da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP, Yarima Abdullah yace, "ya kasance mai sha'awar Chateauroux na wani lokaci, kuma tattaunawa tayi nisa don mallakar kungiyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu