Wasanni

Kocin Super Eagles ya yi watsi da sukar mutane kan kiran Ahmed Musa

Kaftin din Najeriya Ahmed Musa
Kaftin din Najeriya Ahmed Musa REUTERS/Toru Hanai

Mai horar da 'yan wasan Najeriya Gernot Rohr ya yi watsi da sukar da mutane ke yi wa Ahmed Musa na rashin bugawa wata kungiya wasa wajen gayyatar sa kungiyar Super Eagles domin karawa a wasannin da za su yi da kasashen Jamhuriyar Benin da Lesotho.

Talla

Sanarwar hukumar kwallon kafar Najeriya ta ce Musa wanda shi ne Kaftin din kungiyar Najeriya na daga cikin ‘yan wasa 24 da Rohr ya gayyata domin fafatawa a wadannan wasanni guda biyu.

Wasu daga cikin 'yan wasan sun hada da mataimakin kaftin William Ekong da mai tsaron raga Francis Uzoho da dan wasan tsakiya Wilfred Ndidi da ‘dan wasan gaba Victor Osimhen.

Sauran sun hada da John noble, mai tsaron gidan kungiyar Enyimba da Leon Balogun da Kenneth Omeruo da Olaoluwa Aina da Oghenekaro Etebo da Joseph Ayodele-Aribo da Alex Iwobi da Moses Simon da Samuel Chulwueze tare da Abdullahi Shehu da Sadiq Umar.

Najeriya ke matsayi na farko a teburin gasar da maki 8, yayin da Jamhuriyar Benin ke da maki 7 sai kuma Saliyo mai maki 3.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.