Wasanni

Ronaldo ya shirya huce haushinsa a karawar Juventus da FC Porto

Dan wasan gaba na Juventus Cristiano Ronaldo.
Dan wasan gaba na Juventus Cristiano Ronaldo. Isabella BONOTTO AFP

Dan wasan gaba na Juventus Cristiano Ronaldo, ya shiryawa karawarsu da Porto yau Talata karkashin gasar cin kofin Zakarun Turai zagaye na 2 rukunin kungiyoyi 16, wasan da ke zuwa bayan a zagayen farko Juventus din ta sha kaye da kwallaye 2 da 1.

Talla

Karawar ta yau dai na zuwa ne bayan nasarar Juventus da kwallaye 3 da 1 kan Lazio a Asabar din da ta gabata, wasan da Andrea Pirlo ya yi amfani da Ronaldo a matsayin sauyi.

A kalaman mai horar da kungiyar ta Juventus, Andrea Pirlo ya ce wasan na ranar Asabar ya hutar da Ronaldon mai shekaru 35 ne don ya samu hutun iya tunkarar karawar ta yau da karfinsa.

Ronaldo wanda ya lashe gasar cin kofin zakarun Turai sau 5 a tarihi, ana ganin zai iyakar kokarinsa don farke kwallayen na Porto da nufin kai kungiyarsa matakin wasa nag aba, dai dai lokacin da Juventus din ke mafarkin lashe kofin da ake ganin shi ne dalilinta na sayo Ronaldon a 2018.

A cewar Pirlo karawar kai tsaye za su iya bayyanata da wasan Ronaldo ganin yadda ya zaqu tun bayan shan kayensu a karawar ta watan jiya.

Yanzu haka dai Juventus din na matsayin ta 3 ne a teburin Serie A kuma za ta yi wasan na yau ne ba tare da mai tsaron bayanta De Light ba ko da ya ke Chiellini zai kasance cikin wasan na yau.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.