Wasanni

Haaland zai kafa babban tarihi a gasar zakarun Turai- Lopetegui

Haaland mai shekaru 20 tauraruwarsa na ci gaba da haskawa a Turai.
Haaland mai shekaru 20 tauraruwarsa na ci gaba da haskawa a Turai. Martin Meissner Pool/AFP/Archivos

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Sevilla Julen Lopetegui ya yi hasashen cewa dan wasan gaba na Borussia Dortmund Erling Braut Haaland ya iya kafa tarihin mamaye gasar cin kofin zakarun Turai na tsawon shekaru la’akari da irin rawar ganin da ya ke yanzu haka a wasannin gasar, bayan kai tawagar ta sa wasan gab da na kusa da karshe na gasar.

Talla

Lopetegui wanda ke wannan batu bayan Haaland ya ratata musu kwallayen da ya yi waje da tawagarsa ta Sevilla daga cikin gasar ta zakarun Turai, ya ce sun yi rashin sa’ar haduwa da dan wasan mai kishirwar kai tawagarsa ga lashe kofin.

Yayin wasan na jiya dai kwallaye 3 Haaland ya zura ko da ya ke na’urar taimakwa alkalin wasa ta VAR ta soke guda, yayinda aka tashi wasa Dortmund ana da 3 Sevilla na da biyu kwatankwacin yadda suka yi a haduwarsu ta farko.

kocin na Sevilla ya ce a tarihin gasar cin kofin zakarun Turai babu wani dan wasa da yayi shigar sauri wajen zura kwallaye a gasar da karancin shekaru kamar Haaland, wanda ken una da yiwuwar ya shafe tarihin wadanda suka gabace shi.

Haaland dan Norway mai shekaru 20, zuwa yanzu kwallaye 20 ya zura a wasanni 14 da ya buga cikin gasar ta cin kofin zakarun Turai wanda ke mayar da shi dan wasa mafi karancin shekaru da ya taba zura makamantan kwallayen.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.