Wasanni

Liverpool ta lallasa RB Leipzig bayan jerin rashin nasara a Firimiya

'Yan wasan Liverpool bayan tashi wasa.
'Yan wasan Liverpool bayan tashi wasa. Bo Amstrup Ritzau Scanpix/AFP/Archives

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta yi nasarar sake lallasa RB Leipzig da kwallaye 2 da nema a wasansu na jiya da ke matsayin haduwa ta biyu a zagayen kungiyoyi 16 na gasar cin kofin zakarun Turai, kwallayen da suka zama kari kan guda biyu da tawagar ta Ingila ta zurawa Leipzig tun a haduwar farko.

Talla

Liverpool wadda ta samu kwallayenta biyu ta hannun ‘yan wasanta na gaba Mohamed Salah na Masar da Sadio Mane na Senegal kungiyar ta sake samun karsashin tunkarar zagayen gab da na kusa da karshe dai dai lokacin da mafarkin kare kambunta na Firimiya ya subucewa mata, sakamakon jerin rashin nasarar da ta ke a gasar inda yanzu ta ke matsayin ta 8 bayan doka wasannin 28.

Mai horar da kungiyar ta Liverpool, Jurgen Klopp da ke yabawa ‘yan wasan na sa kan irin hazakar da suka nuna a karawar duk da cewa sai bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne suka iya zura kwallayen, ya ce sauye-sauyen da suka samar a zubin ‘yan wasan ya taimaka matuka.

 A cewar Klopp dan wasan tsakiya na tawagar Fabinho ya yi rawar gani a karawar ta jiya bayan sauya masa waje daga inda ya saba rikewa tun bayan dawowarsa daga jinya.

A juma’ar makon gobe ne Liverpool za ta san kungiyar da za ta kara da ita a rukunin kungiyoyi 8 na gasar bayan UEFA ta fitar da sabon jadawali.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.