Wasanni - Ingila

Pulisic yayi barazanar rabuwa da Chelsea saboda Tuchel

Christian Pulisic dan asalin kasar Amurka dake wasa a kungiyar Chelsea.
Christian Pulisic dan asalin kasar Amurka dake wasa a kungiyar Chelsea. AP - Frank Augstein

Fitaccen dan wasan gaba a Turai dake Chelsea Christian Pulisic yayi barazanar rabuwa da kungiyar, saboda rashin bashi damar buga wasanni a karkashin sabon kocinsu Thomas Tuchel.

Talla

Jaridar Sun da ake wallafa ta a Birtaniya ta ruwaito cewar, tuni Pulisic ya tuntubi dillalansa kan matsalar da yake fuskanta da kuma aniyarsa ta neman sauyin sheka.

Har yanzu dai Tuchel bai sanya Pulisic cikin tawagar farko ta ‘yan wasansa ko da sau guda ba, tun bayan da ya karbi ragamar horas da kungiyar Chelsea daga hannun Frank Lampard.

Rahotanni da suka soma bulla a ranar Talatar da ta gabata sun ce tuni Manchester United da Liverpool suka soma tuntubar wakilan Christian Pulisic da darajarsa yanzu haka a duniyar kwallo ta kai fam miliyan 57.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.