Wasanni

Barcelona ta soma tuntubar kulla yarjejeniya da Aguero

Dan wasan gaba na Manchester City Sergio Aguero.
Dan wasan gaba na Manchester City Sergio Aguero. AP - Scott Heppell

Kungiyar Barcelona ta soma tuntubar dan wasan gaba na Manchester City Sergio Aguero, wanda yarjejeniyar sa za ta kare ranar 30 ga watan Yunin da ke tafe.

Talla

Har yanzu dai Messi ya ki sabunta yarjejeniyar sa da Barcelona abinda ya haifar da shakku kan makomarsa a kungiyar biyo bayan ficewarsu daga gasar zakarun Turai ranar laraba, bayan rashin nasara a hannun PSG da 5-2.

Sai dai sabon shugaban kungiyar Barcelona Joan Laporta ya bayyana kwarin gwiwar gamsar da Messi ya zauna ta ta hanyar kulla yarjejeniya da Aguero.

Jumillar kwallaye 254 Aguero ya ci wa Manchester City tun bayan fara buga mata wasanni a shekarar 2011, kuma har yanzu shi ne ke rike da tarihin dan wasa daga ketare da ya yi hattrick wato cin kwallaye 3 a wasa 1 sau 12 a gasar Firimiyar Ingila.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.