Wasanni-Gasar Zakarun Turai

Makomar Ronaldo a Juventus ta shiga halin rashin tabbas

Cristiano Ronaldo na kungiyar Juventus.
Cristiano Ronaldo na kungiyar Juventus. AP - Luca Bruno

Rahotanni daga birnin Turin na Italiya sun ce hukumar gudanarwar kungiyar Juventus ta cire Cristiano Ronaldo daga cikin ‘yan wasan da tace bana sayarwa bane.

Talla

Wasu majiyoyi daga kungiyar ta Juventus sun ruwaito cewar matakin na da nasaba da shirin da take na yin garambawul domin fuskantar kakar wasa ta gaba bayan ficewar da ta yi daga gasar Zakarun Turai a zagaye na biyu da ya kunshi kungiyoyi 16.

Juventus ta gaza kaiwa zagayen kwata final ne bayan yin 4-4 a wasanni biyun da suka fafata da FC Porto, inda a zangon farko Porto ta samu nasara da 2-1 a Portugal, a zango na biyu kuma Juventus ta yi nasara da 3-2 a Italiya.

Tauraron Juventus Cristiano Ronaldo yayin fafatawa da takwarorinsa na Lokomotive Moscow, a kasar Rasha.
Tauraron Juventus Cristiano Ronaldo yayin fafatawa da takwarorinsa na Lokomotive Moscow, a kasar Rasha. AP - Pavel Golovkin

Tuni ya tabbata kocin kungiyar Andrea Pirlo zai cigaba da rike mukaminsa, gami da bayyana Matthijis de Ligt, da Szczesny daga cikin jerin ‘yan wasan da za su ci gaba da kasancewa tare da Juventus, sai dai babu tabbas kan makomar Cristiano Ronaldo.

Gabannin ficewarsu daga gasar zakarun turan dai dama was una gunagunin cewar sayen Cristiano Ronaldo da Juventus tayi bai kare ta da komai ba, musamman ma dangane da gasar Zakarun Turai da tayi sayi dan wasan domin lashe kofinta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.