Wani hannin ga Allah baiwa ne - Ronaldo

Dan wasan  gaban Juventus a kasar Italiya
Dan wasan gaban Juventus a kasar Italiya Isabella BONOTTO AFP

Fitaccen ‘dan wasan Juventus Cristiano Ronaldo ya bayyana cewar ko gezau basa yi dangane da koma bayan da suka samu a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai, yayin da suka mayar da hankalin su kan gasar Serie A wadda zasu kara da kungiyar Cagliari a gobe lahadi.

Talla

A sakon da ya aike ta kafar Instagram, Ronaldo yace ba’a karya kashin bayan zakaru na gaskiya, saboda haka yanzu sun mayar da hankalin su kan wasan Cagliari da kofin kalubalen Italia da kuma sauran wasannin da suka rage musu a wannan kaka.

Dan wasan da ya fito daga kasar Portugal yace abin dubawa a rayuwa shine yadda ka murmure daga koma bayan da ka samu da kuma sake tsayawa da kafafuwan ka, maimakon cigaba da korafi kan matsalolin da ka fuskanta.

Makomar Ronaldo ta zama abin cece kuce tun bayan ficewar kungiyar su ta Juventus daga gasar cin kofin zakarun Turai, wanda ‘dan wasan ke sahun gaba wajen jefa yawan kwallayen da suka fi na kowa a tarihi, sakamakon 134 da ya zirara shi kadai, kana kuma ya lashe kofin gasar har sau biyar.

Dan wasan yace ba’a share tarihi ko kadan, saboda yadda yake zama zanen dutse da kuma abin nuni ga masu zuwa nan gaba, kan rawar da suka taka a matsayin dunkulalliyar kungiyar masu neman kafa tarihi. Yanzu haka kungiyar Juventus ke matsayi na 3 a teburin Serie A wadda Inter Milan ke jagoranci, yayin da kuma ta samu damar zuwa wasan karshe na cin kofin kalubalen Italia.

 

 

 

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.