Wasanni - Ingila

Ban ga amfanin kai gwiwa kasa don kyamar wariyar launi ba - Zaha

Dan wasan gaba na kungiyar Crystal Palace Wilfred Zaha.
Dan wasan gaba na kungiyar Crystal Palace Wilfred Zaha. © AFP

Dan wasan gaba na kungiyar Crystal Palace Wilfred Zaha, ya zama dan wasan dake gasar Firimiyar Ingila na farko da ya daina durkusawa kan gwiwarsa guda 1 dake nuna kyamar dabi’ar nuna wariyar launi, matakin da aka soma dauka cikin watan Yunin shekarar bara.

Talla

Zaha ya dauki matakin ne, a yayin da Crystal Palace ke shirin fafatawa da West Brom a ranar Asabar da ta gabata, wasan da Palace ta samu nasara da 1-0.

Tun a watan da ya gabata, yayin zantawa da jaridar Financial Times, Zaha ya sha alwashin daina kai gwiwarsa guda 1 kasa da ‘yan wasa ke yi da nuna kyamar wariyar launi, biyo bayan kashe bakar fata Gorge Floyd da wani dan sandan Amurka farar fata ya yi a birnin Minneapolis, cikin watan Mayun shekarar 2020.

Tauraron na Crystal Palace ya ce a halin yanzu bai ga amfanin ci gaba da durkusawa kan gwiwa 1 ba, domin kuwa har yanzu ba a daina cin zarafin ‘yan wasa ko nuna musu wariyar launi ba, yayin buga wasanni a nahiyar Turai.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.