Wasanni

Chelsea za ta saida 'yan wasanta 5 domin sayen wasu fitattu 3

Kocin Chelsea Thomas Tuchel, Tammy Abraham daya daga cikin 'yan wasan da rahotanni suka ce yana shirin sallama.
Kocin Chelsea Thomas Tuchel, Tammy Abraham daya daga cikin 'yan wasan da rahotanni suka ce yana shirin sallama. AP - Dave Thompson

Majiyoyi da kungiyar Chelsea sun ce ta soma shirin sayar da ‘yan wasan ta guda 5, domin samun damar sayen fitattun ‘yan wasan da suka hada da Erling Haaland, Gini Donnarumma da kuma Kingsley Coman na Bayern Munich.

Talla

Kiyasin da ya tabbata cewar fitattun ‘yan wasan da za su lakumewa Chelsea sama da euro miliyan 200 ne ya tilastawa kungiyar zabar wasu daga cikin ‘yan wasan ta da za ta saida, domin kaucewa karya dokar kashe kudade fiye da wadanda ke shigo mata, wato ‘Financial Fair Play Rule’ a turance.

Jaridar Daily Star dake Birtaniya ta ruwaito cewar ‘yan wasan da Chelsea za ta saida sun hada da Fikayo Tomori, Christian Pulisic, Tammy Abraham, Emerson da kuma Kepa.

Yanzu haka wasanni 12 Chelsea ta buga ba tare da yin rashin nasara, tun bayan da Thomas Tuchel ya karbi aikin horas da ‘yan wasan kungiyar daga hannun Frank Lampard.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.