Wasanni

Ronaldo na Portugal ya goge tarihin da Pele na Brazil ya kafa a kwallo

Cristiano Ronaldo na Portugal da Pele na Brazil a wani hoton hadi.
Cristiano Ronaldo na Portugal da Pele na Brazil a wani hoton hadi. © Marco Alpozzi/AP & AP - Montage RFI

Tsohon tauraron ‘dan wasan kwallon kafa na duniya, Pele na Brazil ya aike da sakon taya murna ga Cristiano Ronaldo na Portugal bayan zuwa kwallaye 3 a karawar da Juventus da Cagliari wanda ya bashi damar zama dan wasa mafi zura kwallaye tare da zarce yawan kwallayen da shi Pele ya jefa a zamanin taka ledarsa.

Talla

Jefa kwallaye guda 3 da Ronaldo yayi ya kai adadin kwallayen da ya ci zuwa 770 a rayuwar sa, sabanin 767 da Pele ya jefa lokacin da yayi ganiyar sa.

A sakon sa ta kafar Instagram, Pele ya bayyana rayuwa a matsayin hanyar da kowa ke shatawa kan sa, yayin da yake jinjinawa ‘dan wasan kan bajintar da ya ke nunawa koda yaushe.

Pele ya ce ya na sha’awar wasan Ronaldo kuma yana jin dadin kallon sa lokacin da ya ke wasa kuma wannan ba wani abin boyewa bane, saboda haka ya ta ya shi murnar share tarihin da ya kafa.

A nasa martini, Ronaldo bayan kammala wasan da suka yi da Cagliari ya ce babu wani ‘dan wasa a duniya da bai tashi yana jin tarihin wasan Pele da kwallayen da yaci da kuma nasarorin da ya samu ba, saboda haka yana mai farin cikin samu yawan kwallayen da suka zarce na shi, abinda bai taba mafarki ba a rayuwar sa.

Ronaldo ya ce yana matukar mutunta Pele kan rawar da ya taka da kuma ficen da ya yi, yayin da ya ke cewa zarce shi da yawan kwallaye ba zai share tarihin gudumawar da Pele ya yi a wasan kwallon kafa ba.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.