Kwallon Kafa - Afrika

Dole wata kasar Afrika ta lashe kofin duniya a nan kusa - Motsepe

Sabon shugaban hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afrika Patrice Motsepe.
Sabon shugaban hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afrika Patrice Motsepe. AP - Themba Hadebe

Sabon Shugaban Hukumar Kwallon kafa ta Afirka, Patrice Motsepe ya ce ya zama dole daya daga cikin kungiyoyin kwallon kafa na kasashen dake nahiyar ta lashe gasar cin kofin duniya nan bada dadewa ba.

Talla

Attajirin Afirka ta kudu da ya gaji Ahmad Ahmad sakamakon zaben da akayi a makon jiya, ya sha alwashin sauka daga mukamin sa nan da shekaru 4 masu zuwa muddin Hukumar Kwallon kafa ta nahiyar ta kasa samun cigaba.

Motsepe yace babu dalilin cigaba da nuna fargaba akan gasar cin kofin duniya, domin babu wata nahiya da ta samu cigaba wajen mayar da hankali kan rashin nasarorin da take samu.

Sabon shugaban hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afrika Patrice Motsepe.
Sabon shugaban hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afrika Patrice Motsepe. AP - Themba Hadebe

Ya zuwa yanzu dai babu wata kasa daga Afirka da ta wuce wasan kwata-final a gasar cin kofin duniya, kuma kasashe 3 kacal suka kai wannan mataki a tarihin gasar da suka hada da Kamaru a shekarar 1990 da Senegal a shekarar 2002 da kuma Ghana a shekarar 2010.

A gasar cin kofin duniyar da akayi a Rasha shekaru 3 da suka wuce, anyi waje da wakilan kasashen Afirka biyar bayan zagaye na farko wadanda suka hada da Masar da Morocco da Najeriya da Senegal da kuma Tunisia.

Yayin da yake tsokaci na farko tun bayan nasarar samun shugabancin Hukumar, Motsepe yace yana da yakinin kwallon kafa a nahiyar Afirka za ta bunkasa da dogaro da kan ta, da kuma zama zakara a duniya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.