Wasanni - Croatia

Kocin Dinamo Zagareb yayi murabus bayan samun shi da laifin zamba

Mai horas da kungiyar Dinamo Zagareb Zoran Mamic.
Mai horas da kungiyar Dinamo Zagareb Zoran Mamic. AP - Kerstin Joensson

Mai horas da kungiyar Dinoma Zagareb Zoran Mamic ya ajiye aikinsa, bayan da kotu ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 4 da watanni 8 a gidan yari.

Talla

Mamic ya fuskanci hukuncin daurin ne, sakamakon samunsa da laifin yin rub da ciki kan wani bangare na miliyoyin euron da Tottenham ta biya kungiyar Dinoma Zagareb domin sayen dan wasan ta Luka Modric, har ma da kudaden da suka shafi sauyin shekar wasu ‘yan wasan.

Kungiyar ta Dinamo Zagareb da tayi fice a gasar kwallon kafar Croatia, ta tabbatar da ajiye aikin mai hors da itan ne, a yayin da take shirin karawa da Tottenham a zagayen da ya kunshi kungiyoyi 16 na gasar Europa.

A halin yanzu Damir Krznar ne ya maye gurbin Zoran Mamic, wanda a baya tsohon mataimakin sa ne.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.