Wasanni - Sweden

Zlatan ya janye ritayar da yayi daga bugawa kasarsa wasa

Zlatan Ibrahimovic yayin murnar jefa kwallo a ragar Girka a wasan da suka fafata na gasar cin kofin nahiyar Turai a shekarar 2008.
Zlatan Ibrahimovic yayin murnar jefa kwallo a ragar Girka a wasan da suka fafata na gasar cin kofin nahiyar Turai a shekarar 2008. ASSOCIATED PRESS - Frank Augstein

Tauraron dan wasan kwallon kafar Sweden Zlatan Ibrahimovic zai kawo karshen ritaya daga bugawa kasarsa wasa na shekaru 5, domin shiga karawar da za tayi na wasan neman zuwa gasar cin kofin duniyar da zai gudana a karshen wannan watan.

Talla

Mai koyar da wasan kungiyar Sweden ta kasa Janne Andersson ya sanar da gayyatar dan wasan, wanda shima Zlatan da kan a ya tabbatar da haka a sakon da ya aike ta Instagram mai dauke da shirin dawowarsa.

Sanarwar tana zuwa ne watanni 3 kafin gasar cin kofin kasashen Turai da zai gudana tsakanin watannin Yuni da Yuli.

Zlatan Ibrahimovic.
Zlatan Ibrahimovic. AP - Alvaro Barrientos

Kafofin yada labaran Sweden sun dade suna hasashen dawowar Ibrahimovic bugawa kasarsa wasa amma hukumar kwallon kafar Sweden taki cewa komai kan lamarin, har saida aka bayyana sunansa cikin jerin ‘yan wasa 25 da za su kara da Georgia ranar 25 ga wata da kuma Kosovo ranar 28 ga wata.

Zlatan Ibrahimovic na fama da ciwon jijiyar kafar sa a cikin yan kwanakin nan, amma kuma ana saran ya koma bugawa kungiyar sa ta AC Milan wasa a karawar da za tayi da tsohuwar kungiyar sa ta Manchester United a gasar Europa.

A gasar cin kofin Turai da za’ayi a watan Yuni Sweden zata kara da kasashen Spain da Poland da kuam Slovakia a rukunin E.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.