Manchester City da Real Madrid sun tsallaka mataki na gaba a gasar UEFA
Wallafawa ranar:
Yanzu haka ta tabata kungiyar Manchesterd City ta tsallaka mataki na gaba bayan lalasa Monchengladbach da ci biyu da nema.Real Madrid ta yi waje da Atlanta Bergame da 3 da 1.Wadanan nasarori na baiwa wadanan kungiyoyi damar zuwa wasanni kusa da na karshe a wannan gasa ta cin kofin zakarun Turai.
Wadanan kungiyoyi za su tare da kungiyoyin Liverpool da PSG.
A baya Liverpool ta doke Rb Liepzig da ci 2 da nema,yayinda PSG ta yi waje da Barcalona.
Haka zalika Fc Porto ta tsallaka mataki na gaba bayan samun nasara a fafatawa da ta yi da Juventus de Turin da ci 3 da 2.
A yau Laraba, Bayern Munich za ta kara da Lazio Roma,mu tunatar da masu sauraren mu a haduwar farko tsakanin kungiyoyin biyu Bayern Munich ta doke Lazio Roma da ci 4 da 1.
Zuwa an jima Chelsea za ta fafata da Atletico Madrid, haduwar farko Chelsea ta casa Atletico Madrid da ci 1 mai ban haushi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu