Wasanni - UEFA

An karkare wasannin gasar Zakarun Turai zagaye na 2

Tambarin gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League dake gudana a karkashin hukumar UEFA.
Tambarin gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League dake gudana a karkashin hukumar UEFA. AP - Claude Paris

An kammala buga wasannin gasar Zakarun Turai zagaye na 2 da ya kunshi kungiyoyi 16. 

Talla

Yayin wasannin da aka karkare a ranar Laraba 17 ga watan Maris, Bayern Munich ta samu nasara kan  Lazio da 2-1, sai Chelsea da ta doke Atletico Madrid da 2-0

Kungiyoyi 8 da suka samu nasarar tsallakawa zuwa zagayen wasan kusa da kusa da na karshe na  kwata final, sun hada da Chelsea, Bayern Munich, Manchester City, Liverpool, PSG, Real Madrid, Borussia Dortmund da kuma FC Porto.

Ranar Juma’a hukumar kwallon kafa ta Turai UEFA za ta fitar da jadawalin kungiyoyin da za su kara da juna a zagayen na kwata final.

Taron fitar da jadawalin kuma zai gudana ne a birnin Nyon dake kasar Switzerland.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.