Wasanni

Ronaldo ya baiwa wakilansa umarnin soma tattaunawa da Real Madrid

Cristiano Ronaldo a lokacin da yake haskawa a kungiyar Real Madrid.
Cristiano Ronaldo a lokacin da yake haskawa a kungiyar Real Madrid. AP - Andres Kudacki

Rahotanni daga Italiya sun ce tauraron Juventus Cristiano Ronaldo ya baiwa wakilansa umarnin soma tattaunawa da tsohuwar kungiyarsa ta Real Madrid kan yiwuwar yi mata kome.

Talla

A shekarar 2018 ya raba gari da Madrid inda ya koma Juventus kan euro miliyan 100.

A waccan lokacin Juventus ta kulla yarjejeniya da Ronaldo ne cike da fatan zai bada gagarumar gudunmawa wajen cin kofin gasar zakarun Turai, said ai shekaru uku bayan sayensa hakarsu ba ta cimma ruwa ba, inda a makon jiya FC Porto ta fitar da su daga gasar ta bana a zagaye na 2 da ya kunshi kungiyoyi 16.

Tauraron kungiyar Juventus Criatiano Ronaldo.
Tauraron kungiyar Juventus Criatiano Ronaldo. AP - Manu Fernandez

Ficewar su daga gasar zakarun Turan ce kuma ta karfafa muhawara kan makomar Ronaldo a Juventus, yayin da kuma a gefe guda, kocin Real Madrid Zinaden Zidane ya gaskata rahotannin dake alakanta dan wasan komawa tsohuwar kungiyar tasa.

Gabannin ficewarsu daga gasar zakarun turan dai dama was una gunagunin cewar sayen Cristiano Ronaldo da Juventus tayi bai kare ta da komai ba, musamman ma dangane da gasar Zakarun Turai da tayi sayi dan wasan domin lashe kofinta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.