Wasanni

Kungiyoyin kwallon kafa 7 sun samu tikitin gasar Afrika na 2022 a Kamaru

Hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar Afrika. CAF
Hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar Afrika. CAF © CAFOnline.com

A gasar neman tikitin shiga jerrin kungiyoyi  da za su isa Kamaru a shekara ta 2022 na cin koffin Afrika,kungiyoyi 7 ne yanzu haka aka tabbatar da sun samu wannan dama.

Talla

A jiya laraba an buga wasanni tsakanin kungiyoyi kamar haka:

Burkina Faso ta yi canzaras da Uganda.

Malawi ta doke Sudan ta kudu da ci 1 mai ban haushi.

Rwanda ta lallasa Mozambique da ci 1 mai ban haushi.

Sudan ta doke Sao Tome Principe da ci 2 da nema.

Madagascar ba ta ji da dadi ba a fafatawa da ta yi Habasha ,wacce ta yi mata ruwan kwallaye da ci 4 da nema.

Sai Guinee da ta doke Mali da 1 mai ban haushi.

Bayan wadanan wasanni na jiya laraba,kungiyoyi 7 ne yanzu suka samu tikitin zuwa kamaru daga cikin kungiyoyi 51 bayan da aka cire Chadi daga cikin wannan tafiya.

Kungiyoyin sun hada da Kamaru, Senegal, Aljeria, Mali, Tunisia, Guinee da Burkina Faso.

 

Super Eagles na Najeriya sun yi sakaci Saliyo ta farke kwallaye 4 da suka saka musu a raga.
Super Eagles na Najeriya sun yi sakaci Saliyo ta farke kwallaye 4 da suka saka musu a raga. JAVIER SORIANO / AFP

A yau Alhamis ,zuwa an jima :Comoros -Togo

Sai Afrika ta kudu -Ghana, Kenya Masar.

Ranar juma’a, Niger -  Côte d'Ivoire.

Ranar asabar  Najeriya za ta yi tattaki zuwa Porto Novo na Jamhuriyar Benin don inda za ta faffata da kungiyar kwallon kafar Ecureuil ta jamhuriyar Benin.

Ko Najeriya za ta iya doke yan wasan Jamhuriyar Benin ?

 Muna  dakon amsoshin ku.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.