Wasanni

Kungiyar Leicester City za ta tsawaita kwantiragin Kelechi Iheanacho

Dan wasan Najeriya da ke taka leda da Leicester City Kelechi Iheanacho.
Dan wasan Najeriya da ke taka leda da Leicester City Kelechi Iheanacho. REUTERS

Wasu bayanai sun ce kungiyar kwallon kafa ta Leicester City na shirin tsawaita kwantiragin Kelechi Iheanacho bayan ruwan kwallayen da ya yi mata a wannan kaka ciki har da wadanda ya zura a ragar Manchester United yayin wasan gab da na kusa da karshen gasar cin kofin FA.

Talla

Dan wasan gaban na Najeriya mai shekaru 24 na shirin shiga watanni sha biyun karshe ne a kwantiragin shekaru 5 da ya kulla kulla da King Power a 2017 bayan raba garinsa da Manchester city.

A wasanni 12 cikin 15 ne Leicester ta yi amfani da Iheanacho wanda ya zura kwallaye 7 a wasanni 4 na baya-bayan nan da ya doka.

Jaridun wasanni a Ingila dai sun ruwaito, Brendan Rodgers mai horar da kungiyar kwallon kafar ta Leicester na bayyana bukatar tsawaita kwantiragin dan wasan wanda ya bayyana a mai cike da bajinta.

A bangare guda shi kansa Iheanacho ya bayyana cewa a shirye ya ke ya tsawaita kwantiraginsa da tawagar matukar bukatar hakan ta taso.

Matukar dai Iheanacho ya amince da sabon kwantiragin kenan zai fara albashim Pan dubu 90 kowanne mako banda alawus alawus.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.