Afrika

Cote D'Ivoire ta lallasa Nijar da ci 3 da nema -Kwallon kafa

Hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar Afrika.
Hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar Afrika. © CAFOnline.com

Yayinda Najeriya ke neman maki daya a wannan tafiya da ta yi jamhuriyar Benin inda za ta faffata da Ecureuils a yau asabar  a birnin Porto Novo ,wanda hakan zai bata damar  tabbatar da  shiga gurbin kasashen da za su taka leda a gasar Cin kofin Afrika karo na 33 a Kamaru a shekara ta 2022, yan wasan Cote D’Ivoire wato les Elephants  da suka ziyarci kungiyar kwallon kafar Nijar ,Meina  a jiya juma’a a birnin Yamai sun lallase yan wasan Nijar da ci 3 da nema. 

Talla

Serge Aurier, Maxel Gradel da Wilfried  Kanon  ne suka baiwa Cote D’Ivoire wannan nasara.

Yan wasan Cote D'Ivoire  Max-Alain Gradel da Serge Aurier,
Yan wasan Cote D'Ivoire Max-Alain Gradel da Serge Aurier, AP - Sunday Alamba
Morocco  ta samu nata tikitin shiga gurbin kungiyoyin da za su isa Kamaru a shekara ta 2022 bayan da ta yi canzaras da kungiyar kwallon kafar Mauritania,wacce za ta nemi a nata bangaren nasara a tattaki da za ta yi zuwa Bangui ranar Talata makon sama.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.