Iwobi ya bar sansanin Super Eagles saboda ya harbu da Coronavirus

Alex Iwobi, dan wasan Najeriya.
Alex Iwobi, dan wasan Najeriya. POOL/AFP

Alex Iwobi ba zai samu fafatawa a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar afrika ta afcon da najeriya za ta kara da kasar Lesotho ba bayan da gwaji ya tabbatar da cewa ya kamu da cutar covid-19, kamar yadda wasu jami’an hukumar kwallon kafar kasar suka shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa.

Talla

Kafin wasan  ranar Asabar da Najeriya ta doke Benin da ci daya mai ban haushi  ne aka gano cewa  dan wasan gaban na Everton ya harbu da cutar Corona.

kakakin hukumar tawagar Super Eagles, Babafemi Raji ya ce dan  wasan ya bar sansanin tawagar, kuma kafin barin sansanin, bai nuna wata alama ta rashin lafiya ba.

sau 2 Iwobi ya ci kwallaye a wasannin neman cancantar shiga gasar ta AFCON da za a yi a kasar Kamaru a watan Janairun shekara mai zuwa.

A ranar Talata Najeriya za ta kara da Lesotho a birnin Lagos.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.