Wasanni-Kwallon Kafa

Real Madrid ba ta bukatar Ronaldo a yanzu

Cristiano Ronaldo.
Cristiano Ronaldo. Marco BERTORELLO AFP

Rahotanni na nuni da cewa Real Madrid ba ta bukatar shahararren dan wasan Juventus Cristiano Ronaldo kamar yadda ake ta yadawa a cewar wata jarida wasanni ta kasar Spain, Cuatro. 

Talla

Real Madrid na iya sayar da ‘yan wasa 6 a wannan karo don farfadowa daga masassarar tattalin arziki sakamakon annobar Covid-19, da kuma yi wa tawgarta garambawul, kaamar yadda jaridar Mundo Deportivo ta ruwaito.

Kungiyar na bukatar matasan ‘ya wasan nan da suka shahara, wato  Erling Haaland daga  Borussia Dortmund da Kylian Mbappe na  Paris Saint Germain –kuma tana iya sadaukar da ‘yan wasa 6 don cimma haka.

A game da batun Ronaldo kuwa, rahotanni na nuni da cewa Manchester United da Paris Saint-Germain duk su na da burin dauko shi.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.