Wasanni-Kwallon Kafa

Sergio Aguero zai raba gari da Manchester City a karshen kaka

Sergio Aguero tare da mai horarwa na Manchester City Pep Guardiola.
Sergio Aguero tare da mai horarwa na Manchester City Pep Guardiola. LAURENCE GRIFFITHS POOL/AFP

Dan wasan gaba na Manchester City mafi zurawa kungiyar kwallo, Sergio Aguero na shirin raba gari da tawagar ta sa a karshen wannan kaka bayan karewar kwantiraginsa.

Talla

Sanarwar da kungiyar ta wallafa a shafinta, ta ce Aguero dan Argentina mai shekaru 32 ba zai sabunta kwantiragi da kungiya na wani wa’adi a nan gaba ba.

Dan wasan wanda ya zurawa City kwallaye 257 a wasanni 384 tun bayan komawarsa kungiyar daga Atletico Madrid a 2011, Club din ya bayyana cewa zai kafa mutummutuminsa na girmamawa da shi da Vincent Kompany da David Silva dukkaninsu wadanda suka yiwa kungiyar bajinta.

Aguero wanda ya ciwa City wasanni masu muhimmanci kwallayen da aka fi tunawa da su su ne na kakar 2012 lokacin da ya taimakawa tawagar kai wa ga dage kofin Firimiya na farko cikin shekaru 44, yayinda daga bisani ya taimakawa Club din dage wasu kofunan na Firimiya 3 FA 1 da kuma kofunan Lig 5.

Shugaban kungiyar ta City Khaldoon Al Mubarak ya ce gudunmawar da Aguero ya bai wa kungiyar ba za su misaltu ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.